Ana Fadakar Da Mata Kan Muhimmancin Shayar Da Jarirai Da Nono Zalla

Jariri

Majalisar dinkin duniya tare da hadin guiwar Asusun tallafawa kananan yara UNICEF sun kebe satin farko na watan Augusta don wayar da kan mata masu goyo game da muhimmancin baiwa jariri nonon uwa tsantsa

Karkashin shirin, asibitin dake kula da mata masu ciki da yara, wato PMI ta Damagaram,yana tattara mata su yi hira da su tun kafin satin, kan yadda za su kula da lafiyar yaran su, musamman muhimmancin ba jarirai nono tsantsa a kalla tsawon watanni shida na farko. Haka kuma jami’an asibitin sukan dauki lokaci domin ziyarar mata da kuma fadakar da su a gidajen su

Jami’ai suna daukar sunayen matan da ke shayarwa suna kuma ziyartarsu a gidajensu da nufin tabbatar da aiwatar da wannan tsarin, da kuma ci gaba da kai jarirai awo.

A cikin hirarta da Muryar Amurka, Madame Marie Albashir mai kula da sashen a hukumar kiwon lafiya ta jiha, ta ce bada nono tsantsa yana da muhimmanci bisa la'akari da mace-macen kananan yara, da ciwon nono, sankaran mama da na mahaifa. Ta kuma jadada cewa, yaron da aka bashi nonon zalla a watannin farko baya fama da gudawa da amai kamar sauran yara, haka kuma yakan fi sauran ilimi idan ya girma.

Wasu matan da suke shayar da jariransu da nono tsantsa sun bayanawa muryar Amurka yaran suna cikin koshi lafiya walwala da kuzari.

Saurari cikakken rahoton Tamar Abari daga Damagaram

Your browser doesn’t support HTML5

Shayar da jarirai da nono zalla-3:30"