Litinin ce Jamhuriyar Nijar ta yi zabe da nufion maido kasar kan turbar demokuradiyya,bayan shekera daya tana karkashin mulkin soja.
Shugaban Nijar na yanzu Janar Salou Djibou,wanda baya daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar 10,ya bayyana “gamsuwa da kyakkyawar fata,yayinda yake kada kuri’arsa a Niamey,babban birnin kasar.Ya kira zaben sabon babi ga Nijar,daya daga cikin kasashe mafi talauci da rashin ci gaba.
Janar Salou Djibo ne ya jagoranci juyin mulkin da ya hambare shugaba Mamadou Tandja,bayan ya tilas sake tsarin mulkin kasar da nufin tazarce.Ahalin yanzu shugaba Tandja yana gidan fursina kan zargin cin hanci da rashawa zamanin da shekaru 10 da ya yi yana mulki.
An yi zaben jiya cikin lumana.
Bayan zaben shugaban kasa ‘yan nijar sun kuma kada kuri’ar zaben wakilan majalisar dokoki.