Cibiyar yaki da cutar kurkunu a Africa na tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter yace an fara samun nasarar ganin karshen cutar nan ta kurkunu a nahiyar Africa.
Cibiyar dake da babban ofishin ta anan Amurka, wadda ke sahun gaba na ganin an kakkabe cutar, tace yanzu ana da matsaloli 30 ne na wannan cutar dake wasu kebabbun wurare a kasashen Chadi da Habasha.
A shekarar data gabata,ne aka gano hakan kuma kowace tana da goma shabiyar ne.
Musali a kasar Habasha an samu masu dauke da wannan cutar ce a wurin da yan gudun hijira suke aiki a gundumar Oromia, bayan sun sha ruwan da ba a tace ba daga ruwan kududdufin dake fitowa daga wata masanaanta.
A kasar Mali ko yanzu an kwashe samada watanni 25 ba labarin bullar wannan cutar,
Haka ma a sabuwar kasar Sudun ta Kudu an kwashe sama da watanni 13 ba labarin wannan cutar.
Cibiyar tace wannan nasarar wani abin babban abin yabo ne.
Shi dai wannan cutar na kurkunu baida wani riga kafi babban maganin sa shine ci gaba da ilmantar da mutane muhimmacin tace ruwa kafin asha shi.
Cibiyar tace cutar na kurkunu bai nuna alamu ga mutumin dake dauke dashi har na tsawon shekara guda.