Dubban mutane a biranen Amurka daban-daban, kama daga New York har zuwa jihar California, su na ci gaba da fitowa kan tituna suna gudanarda gagarumar zanga-zagar nuna rashin yardarsu da zaben da aka yi wa Donald Trump a matasyin sabon shugaban Amurka na 45 a zaben da aka gudanar ranar talatar da ta gabata.
WASHINGTON DC —
Aksarin masu zanga zangar dai duk dalibbai ne Bakaken Fata da Latinawa.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun bayyana yadda bakin haure ke ci gaba da fafatikar neman wurin zama da ci gaba da rayuwarsu amma suna da damuwa gameda irin kalaman da suke jin suna fitowa daga bakin Trump, kuma suna da fargaba gameda matsayinsa akan mutane irinsu, sannan suna zarginsa da cewa yana kyamar mutane masu wani launin fata da ba irin nasa ba.
Daga cikin biranen da aka gudanarda tarukkan zanga-zangar akwai harda biranen New York, San Fransisco, Los Angeles, da Oakland. A biranen da dama masu zanga-zangar sun toshe manyan hanyoyi, wasu wuraren ma (kamar Oakland) har da kone-kone.