Wasu mazauna kauyen Shinkai na karamar hukumar Wukari da ke jihar Taraba, sun fara guduwa su na barin gidajen su, bayan barazanar da aka yi musu na cewar za a kawowa kauyen na su hari, saboda zargin da ake yi musu na kashe wani jami'in soja.
Mazauna garin sunce wasu mutane sanye da kaki sun zo kauyen nasu ranar Lahadi, inda suke zargin cewa an kashe musu dan uwansu.
Shiko Mista Simon Dogari, kwamishinan yada labarai na jihar ta Taraba, ya ce sun samu rahoton cewa akwai matsala a kauyen Shinkai, bayan rikicin da aka yi tsakanin makiyaya da kuma wasu sojoji da ake tunanin 'yan "Operation Whirl Stroke" ne, rikicin ya sa an kashe daya daga cikin sojojin.
Kwamishinan ya ce shima yana mamakin yadda aka yi sojojin da aka tura su aiki jihar Binuwai, su ke shigowa jihar Taraba. Ya ce amma zuwa yanzu, an saka shugaban karamar hukumar Wukari, akan ayi bincike kwakkwara akan lamarin.
Kawo yanzu itama rundunar 'yan sandan jihar ta bakin kakakinta David Misal tace tana bincike kan wannan batu.
Ga rahoton Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5