Ana Cigaba Da Muzgunawa Fararen Hula A Myanmar

Wata babbar jami’ar kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya dake gudanar da bincike a kasar Myanmar, tace ba mamaki “sojoji sun take haddin bil’adama” a yammacin kasar, da sunan cewa wai suna kokarin rufe kafofin sadarwar Internet.

A jiya Litinin ne Yanghee Lee, ta rubutawa hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, cewar an rufe duk wasu hanyoyin sadarwar internet a garuruwan Rakhine dake makoftaka da jihar Chin, yankin da sojoji ke yaki da ‘yan ta’adda na kungiyar Arakan tun a shekarar da ta gabata.

Lee, ta kara da cewar taji kishin-kishin cewar sojoji na binciken harkokin da suka shafi yanar gizo a yankin, wanda hakan na iya zama hanyar muzgunawa fararen hula a yankin.

Kamfanin sadarwa na Telenor Group yace an dakatar da yanar gizo ne a yankin, bisa umurnin ma’aikatar sufuri da sadarwa, bisa dalilin cewar ana amfani da yanar gizon wajen aikata wasu miyagun ayyuka.