Ana Cigaba da Musayar Kalamai Tsakanin PDP da APC

Ibrahim Hassan Dankwambo, gwamnan jihar Gombe.

Biyo bayan harin da matasa suka kaiwa gwamnan Gombe Dankwambo a Kashere garin tsohon gwamnan jihar Danjuma Goje, PDP da APC suna mayar da kalamai a tsakaninsu inda suke nunawa juna yatsa akan abun da ya faru.

Kowane bangaren na azawa daya bangaren laifin neman tada zaune tsaye a kemfen din nan domin zaben watan Fabrairu.

APC dai wacce ta tuna yadda aka jefawa kakakin majalisar wakilan Najeriya barkonon tsohuwa domin ya canza sheka, ta bukaci 'yansanda su sako wasu 'yan adawa da suka kame a Gombe. An kamasu ne bayan da matasa suka jefi tawagar motocin gwamnan yayin da ya kai ziyara garin Kashere.

Jami'in labarun gwamnan, Junaidu Muhammad yace 'yan adawa sun kai hari ne domin neman hallaka gwamna Dankwambo. Yace yaran tsohon gwamnan jihar suka fito da makamai kala-kala da suka hada da bindiga suna harbe-harbe.

Kodayake Junaidu Muhammad bai ga bindiga da idanunsa ba amma ya hakikance matasan sun yi anfani da bindiga domin injishi, akwai alamar harbi a jikin motar gwamna Dankwambo. Yace su basu mayarda martani ba haka suka fita daga garin. Junaidu ya zargi tsohon gwamnan jihar Haruna Goje da shirya harin wannda ya kira bala'i.

Inji Junaidu Muhammad duk da cewa Kashere garin Danjuma Goje ne amma mutanen garin basa goyon bayansa. Wai suna goyon bayan gwamna Dankwambo ne dari bisa dari. Wai sojojin haya aka dauko suka jajjefi gwamnan.

A cikin zantawar da yayi da manema labaru a Abuja dan takarar kujerar gwamnan Gombe din a karkashin inuwar APC Muhammadu Inuwa Yahaya ya musanta ikirarin. Idan 'yansanda sun kama mutane a Kashere ina hujjarsu? Ina makaman da aka ce suna dauke dasu har suka yi anfani dasu? Harkar dimokradiya ta bada dama ga kowa ya fadi ra'ayin bakinsa. Ba'a ga makami ba kuma a kama cewa akwai makami, ba daidai ba ne.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Cigaba da Musayar Kalamai Tsakanin PDP da APC 2' 57"