Ana Cigaba Da Bukukuwan Karamar Sallah

  • Ibrahim Garba

Sallar Eid el Fitr

Musulmi a fadin duniya na cigaba da shagulgulan Karamar Salla, wadda aka yi bayan kammala azumin watan Ramadan a ranar daya ga watan 10 wato Shawwal.

Musulmi a fadin duniya na cigaba da gudanar da shagulgulan karamar Sallah ko Eid el Fitr, wadda ta kawo karshen azumin watan Ramadan.

Wadannan hidindimun na ibada dai su ne cikamakon ayyukan Ramadan, lokacin da Musulmi kan yi azumi tun daga asuba zuwa faduwar rana a tsawon watan na Ramadan.

Dama ranar daya ga wata na 10 a kalandar Musulunci wato Shawwal, ita ce karamar Sallah wato Eid el Fitr.

A kasar Afghanistan, Shugaba Mohammad Ashraf Ghani jiya Jumma'a ya yi tayin tsagaita wuta na kwanaki uku da kungiyar Taliban a wani jawabi ga kasar na jaddada ranar Sallah. Wa'adin tsagaita wutar dai zai kai zuwa gobe Lahadi, kodayake ya so wa'adin ya ma fi haka tsawo.