Samun ingantaccen ilimi a Najeriya abu ne da ke ci gaba da sanya shakku a zukatan al’ummar kasar duba da yadda gwamnatoci a matakai daban-dabam ake dangantasu da nuna halin ko in kula akan makarantun gwamnati da akasarin yaran masu karamin karfi ke zuwa.
A yayin da ake ci gaba da neman mafita ga yadda za a sake bude makarantun boko ba tare da sanya daliban kasar cikin hadari ba sakamakon ci gaba da yaduwar annobar coronavirus, ko menene makomar karatun allo bayan haramta barace-barace da wasu gwamnonin arewa suka yi a baya?
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya ce ilimin allo ya dade tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, don haka yanzu dole ne a duba a ga yadda zasu amfana da tsarin ilimin gwammnati kuma ta yadda ilimin zai tafi da zamani.
A wani bangare kuwa, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya ce bisa ga dokar Najeriya ya kamata kowanne yaro ya je makarantar boko amma banda yawon bara. Ya kara da cewa kowacce jiha za ta nemi wata dabara ta yadda yaran za su zama masu alfanu ga al’umma nan gaba.
Shi ma shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewa, Nastura Ashir Sharif, ya yi karin bayani akan makomar karatun allo. Ya ce idan da gaske za a maida tsarin makarantun allo zuwa na boko lallai abu ne mai alheri.
Masana a faninin karatun allo na ci gaba da kokawa akan yanayin tafiya da tsarin almajiranci a kasar inda suka bukaci gwamnati ta bada gudunmowa wajen farfado da tsohon tsarin karatun allo da aka sani kafin zuwan turawan mulkin mallaka tare da ba duk wanda ya karanci ilimin arabiyya fifiko wajen bada aiki kamar sauran takwarorinsu na boko.
Abun jira a gani shi ne yadda gwamnonin arewa zasu aiwatar da tsarin hada karatun allo da na boko kamar yadda suka yi alkawari.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf.
Your browser doesn’t support HTML5