A yayin da ake ta cece kuce kan raba masarautar Kano zuwa gida biyar, Farfesa Samuel Zalanga wani dan Najeriya mazaunin kasar Amurka, kwararre a fannin ilimin rayuwar dan adam da zamantakewa, ya yi tsokaci akan matakin da majalissar Jihar Kano ta dauka.
A cikin hirarsu da Grace Alheri Abdu, Farfesa Zalangal ya bayyana cewa, abunda yafi muhimamacin a Arewacin Najeriya shine, hanyoyin da shuwagabanni zasu bi domin Inganta rayuwar talakawa da duk al’ummar kasar. Ya ce, ya kamata shuwagabbanni kamar su gwamnoni da sarakuna su hada kai suyi aiki tare domin su kawo ci gaban da al’ummar arewacin Najeriya zasu amafana, ba wai abinda zai kawo rikici da raba kawunan jama’a ba.
Idon muka duba tarihin masarautar Kano an kafata ne tun lokacin Jihadi a shekarar alif dari tara da hudu, 1804. Bai kamata ace a yanzu anzo an canja wannan tsarin ba.
Ya kara da bada Misali da Kasar Malaysia wadda ta kasance cikin kasashe masu tasowa amma ta samu ci gaba sosai saboda hadin kan al’ummar kasar.
Daga karshe ya yi ga Al’ummar Najeriya da su hada kansu domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali domin sune babban ginshikin tattalin arzikin kasa.
Ga Karin Bayani a Cikin Sauti.
Your browser doesn’t support HTML5