Ana Ci Gaba da Takaddama Akan Makomar Matar Shugaban Zimbabwe

Grace Mugabe matar shugaban kasar Zimbabwe

Biyo bayan korar da shugaba Mugabe ya yiwa mataimakinsa ana kyautata zaton shugaban zai nada matarsa ta zama mataimakinsa saboda can baya ta nuna sha'awar zama mataimakiyar shugaban kasar

Ana ta kara takaddama kan makomar matsayin matar Shugaban kasar Zimbabbwe, bayan da Shugaba Robert Mugabe ya jinjina ma ta a wani gangamin siyasa jiya Laraba, wanda hakan ya nuna alamar ita ce zai goyi bayan ta gaji Mataimakin Shugaban kasar da ya kora kwanan nan. A Afirka ta kudu, wata kungiya ta tsoffin sojojin da su ka fafata a yakin neman ‘yancin kan Zimbabwe sun ce za su kalubalanci Mugaba a siyasance badi – ta yadda za su maida korarren mataimakin Shugaban kasar dan takararsu..

Jam’iyyar ZANU-PF mai mulki za ta yanke shawararta a hukumance ne a wani babban taron jam’iyyar da za a yi a tsakiyar watan Disamba.

A halin da ake ciki kuma, Chris Mutsvangwa, Shugaban kungiyar tsoffin sojojin Zimbabwe mai fada aji, ta kai ziyarar a makwabciyar kasar ta Afirka Ta Kudu jiya Laraba, su na kiran da Mataimakin Shugaban kasar Zimbabawe din da aka kora kwanan nan Emmerson Mnangagwa ya zama dan takarar gamayyar jam’iyyun da za su kalubalanci Mugabe a zaben badi.