Batun sake kame shugaban kungiyar samar da sabuwar kasar Biafra ta IPOB, wato Nnamdi Kanu naci gaba da kawo rarrabuwar kawuna a jihohin kudu maso gabashin Najeriya.
Yunkurin sake kame Kanu din ya biyo bayan karya dukkan sharuddan da kotu ta gitta masa ne gabanin bada belin sa.
Wani daga cikin masu raayin kafa wannan sabuwar kasar ta Biafra mai suna Obinna Ozokwu ya shaida wa wakilin Muryar Amurka, Alphosus Okoroigwe, cewa wanda duk yayi yunkurin kama Kanu to yakwana da sanin cewa bai nemi zaman lafiya ba.
Obinna yace ba shakka idan aka sake kama shi to Najeriya zata girgiza domin kuwa zasu yi fada sosai har sai sunga an sako shi.
Shima Victor James Oyebuwa ya ce bai dace a kama Kanu ba domin kuwa yanzu lokacin demokaradiiyya ne da ya baiwa ‘yan kasa ‘yancin fadin albarkacin bakin su.
Sai dai da aka tambaye shi akan ko me yake ganin zai faru idan an kama Nnamdi Kanu, sai Oyebuwa ya amsawa da cewa ba wani abu da zai faru domin gwamnati ce take da iko akan dukkan ‘yan kasa.
Ga dai Alphonsus Okoroigwe da Karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5