Ana Ci Gaba Da Mummunar Danniya A Iran

Kungiyar Amnesty International ta ce, hukumomi a Iran na ci gaba da “mummunar danniya,” biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a duk fadin kasar wadda ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 304.

A wata sanarwar da hukumar ta fitar a yau Litinin, kungiyar mai kare hakkin bil-Adama wacce ke da hedkwata a birnin London, ta ce hukumomin kasar suna “kame irin na mugunta,” inda su ke damke dubban masu zanga-zanga, ‘yan jarida, ‘yan rajin kare hakkin bil adama, da dalibai, da “nufin hana su kalubalantar mulkin kama-karya,” da Iran ke yi.

A tsakiyar watan Nuwamba ne zanga-zangar ta barke, bayan da gwamnati ta yi shelar karin farashin mai a daidai lokacin da ake fama da radadin takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasar.