Ana Ci Gaba Da Ceto Mutanen Da Gida Ya Rufta Da Su a Legas

Wannan hoto yana nuna yadda aka ceto daya daga cikin yaran da gida ya rubta da su a ranar 13 Maris, 2019.

Jami’an ba da agajin gaggawa a Najeriya sun ce, akalla mutum takwas ne suka mutu sannan aka kubutar da wasu 40, bayan da wani gini ya rushe a jihar Legas.

Baya ga haka, akwai yara da ba a san adadinsu ba, wadanda suka mutu ko kuma suka makale a cikin baraguzan benen mai hawa uku, wanda ke dauke da wata makarantar Firaimare.

Wasu da suka shaida hadarin, sun ce makarantar a benen karshen take, kuma akwai akalla dalibai 100 a cikinta.

Motocin daukar marasa lafiya da na kashe gobara tare da motar katapila, sun hallara domin gudanar da ayyukan ceto, wandanda ake ta yi har zuwa cikin daren jiya.

Rushewar ginin ta faru ne a unguwar da ake kira Ita-faji da ke yankin tsbirin da ake kira, Lagos Island, yankin da shi ne dadadde a jihar.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya lashe zabe a kwanan nan, ya nuna alhininsa kan wannan lamari a shafin Twitter, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar ta Legas, da ta dauki matakan kare aukuwar irin wannan hadari.