Har yanzu ana samun takun saka tsakanin ‘yan majalisar dattawan kasar dangane da kasafin kudin 2018 wanda tuni shugaba Muhammad Buhari ya riga ya rabtabawa hannu.
Sanatan dake wakiltar mazabar yammacin jihar Nasarawa Abdullahi Adamu ya ce akwai abun dubawa akan korafin cushe da aka zargi majalisar kasa da yi.
Sanata Abdullahi Adamu yana son shugaban kasa da ofishin dake kula da kasafin kudi su baza kolin abun da aka kawo masu daga majalisa. A bayyana ayyukan da aka kara da basa cikin kasafin domin a san inda aka sasu. A yiwa ‘yan Nigeria cikakken bayani kowa ya gane.
Amma shugaban kwamitin kula da kasafin kudi na majalisar dattawa Sanata Danjuma Goje ya yi bayanin abun da ya sa suka yiwa kasafin kudin garambawul bayan da shugaban kasa ya mika masu.
Na farko ya ce tashin farashin man fetur a kasuwar duniya na cikin dalilin da ya sa suka yi gyara. Misali, shugaban kasa da ma’aikatansa sun tsayar da farashin mai na kowace ganga akan dalar Amurka 45 amma su ‘yan majalisa sun san farashin ya fi haka. Bayan sun yi shawara da shugaban kasa da mukarrabansa sun kara dala shida. Wannan shi ya sa aka samu karin kudi da majalisar ta yi anfani dashi wajen kawar da abubuwan da suka damu mutane. Ma’aikatatun hanyoyi da na kiwon lafiya sun samu kari da zai taimakesu yiwa al’umma aiki.
Danjuma Goje yace dama can akwai doka da ta ce kashi daya cikin dari na kasafin kudin kasar za’a tanadarwa kiwon lafiya. A can baya ba’a kiyaye dokar ba amma a wannan karon majalisa ta ga ya dace su yi aiki da dokar.
Wani tsohon dan majalisar wakilai Dr. Haruna Yarima ya ce dole ne a sake fasalin aikin ‘yan majalisa idan ana son a kawar da cin hanci da rashawa saboda kwana kwanan wani dan majalisar ya fito ya fada cewa kowane dan majalisa ana bashi Nera miliyan 13 a wata a matsayin alawus din aiki. Yana mamaki irin aikin da suke yi har za’a biya kowanensu makudan kudi haka.
A saurari rahoton Medina Dauda
Your browser doesn’t support HTML5