Ana Ci Gaba Da Ce-Ce-ku-ce Akan Kungiyoyin Tsaro Masu Zaman Kansu

A daidai lokacin da shiyoyin kudu maso kudu, da kudu maso gabashin Najeriya ke kokarin kafa nasu kungiyoyin tsaron, wata takkaddama ta kunno kai a arewacin kasar inda gwamnonin arewa da ma shugabannin addinai suka fito karara suka ce ba sa goyon bayan kungiyoyin, har da wanda gamayyar kungiyoyin matasan arewa wato CNG su ka kafa wacce ake kira "Shege Ka Fasa."

Amma manyan 'yan siyasa daga shiyar arewa irin su Sanata Abdullahi Adamu, ya ce yana goyon bayan matasan dari bisa dari domin a ganin sa abubuwa ba sa tafiya daidai musamman a fannin mukamai da babu 'yan arewa sosai.

Shi ma Sanata Emmanuel Bwacha daga Jihar Taraba ta Kudu ya ce idan an yi la'akari da halin da kasa ke ciki na rashin tsaro ya kamata a bar shiyoyi su kafa nasu kungiyoyin domin su kare kansu, kuma yin haka ba wai za su yi aiki daban da jami'an tsaron kasa ba ne amma za su yi aiki tare kuma ta yadda doka ta tanada.

To sai dai bangaren Majalisar wakilai a ta bakin mai magana da yawun su Benjamin Kalu, su na kira ne ga shugabannin hukumomin tsaro akan su yi murabus.

Amma ga mai nazari akan al'amuran yau da kullum Dakta Suleiman Shu'aibu Shinkafi, bai kamata mahukuntan kasar su bari a yi irin wadanan kungiyoyin ba domin tsaron al'umma ya rataya ne a wuyan su, ya kuma bada shawarar a kafa wata kungiya mai karfi ta kasa da za ta taimaka wa 'yansanda da jamia'an tsaron kasa.

Abin jira a gani shi ne irin tasirin da kungiyoyin za su yi wajen tabbatar da tsaro a kasar baki daya.

A saurari rahoto cikin sauti daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Ci Gaba Da Ce-Ce-ku-ce Akan Kungiyoyin Tsaro Masu Zaman Kansu