Fadar shugaban Najeriya ta kare nadin da shugaba Muhammadu Buhari yayi ma ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar a matsayin darekta-janar na hukumar leken asiri ta Najeriya, wadda a cikin 'yan kwanakin nan ta shiga cikin rikici.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yace masu yin adawa da nadin Ambasada Abubakar, su na amfani da kafofin yada labarai wajen baza karairayin cewa shi ba dan Najeriya ba ne.
Malam Garba Shehu yace da gaske ne an haifi sabon babban darektan hukumar ta NIA a kasar Chadi, ya kuma yi karatun firamare a can, amma kowa ya san cewa shi dan Jihar Katsina ne, kuma a nan ya komo ya kammala karatunsa.
Game da korafin da masu adawa da nadin suke yi na cewa bai cancanta ba, yace Ambasada Abubakar yayi aiki har ya kai matsayin mataimakin darekta a cikin ita wannan hukuma ta NIA, mukamin da ya rike na tsawon shekaru 4. Yace da aka zo jarrabawa ma, Ambasada Abubakar ya samu hayewa zuwa ga mukamin darekta, amma ya hakura da karbar kujerar ya bar ma wasu.
Malam Tijjani Isa na wata kungiya dake kiran kanta Patriotic Front of Nigeria, yace wadannan bayanai da gwamnatin ke bayarwa game da nadin Ambasada Abubakar, su na kara dagula lamarin ne, domin a cewarsa, a yayin da Malam Shehu Garba ke fadin cewa lallai a Chadi aka haifi sabon darekta janar din, shi kuwa fada yayi cikin takardunsa na aiki cewa a Katsina aka haife shi.
Ya kara da cewa a bisa tsari, dole ne duk wanda zai zamo darekta janar na wannan hukuma, ya kasance daya daga cikin darektocinta. Shi kuwa Ambasada Abubakar, yayi ritaya daga hukumar, kuma a lokacin da yayi yana matsayin mukaddashin darekta ne.
Ga cikakken bayani a wannan rahoto na Umar Faruk Musa daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5