Ana Ci Gaba Da Ayyukan Ceto A Turkiyya, Da Siriya, Inda Adadin Mace Mace Sanadiyyar Girgizar Kasa Ya Haura 5,000

Ayyukan ceto a Turkiyya

Hankalin duniya ya karkata ga kai dauki Turkiyya da Siriya, inda mutane sama da 5,000 su ka rasu sanadiyyar girgizar kasa.

Masu ayyukan ceto a kasar Turkiyya da Syria, na ci gaba da kokarin kubutar da wadanda baraguzan gine-gine suka rufta a kansu, bayan wasu jerin girgizar kasa da suka auku da safiyar Litinin yayin da adadin mutanen da suka mutu a tsakanin kasashen biyu ya doshi dubu biyar.

Malam Ali Ya’u, dan Najeriya ne da ke karatun digirin-digirgir a Santanbul babban birnin kasar ta Turkiyya, ya kuma yi wa Mahmud Lalo karin haske kan halin da ake ciki a yinin yau Talata.

Ya ce wannan ce girgizar kasa mafi muni a tarihin Turkiyya, inda ya bayyana cewa an yi ta girgizar kasar da kuma hucin girgizar kasar akai akai.

Malam Ali ya ce adadin mace mace na ta karuwa yayin da kuma masu ayyukan ceto da hukumomi ke ta yin abin da su ke iyawa, duk da cikas din da dusar kankara ke kawowa.

Saurari cikakkiyar hirar Mahmud da Malam Ali.

Your browser doesn’t support HTML5

Bayani Kan Girgizar Kasar Turkiyya.mp3