Shugabannin Kasashen Duniya Suna Ci Gaba Da Aikewa Da Sakonnin Ta'ziyyar Mutuwar Tsohon PM Isra'ila Ariel Sharon.

Tsohon PM Isra'ila Ariel Sharon.

Tsohon PM Isra’ila Ariel Sharon ya mutu yana da shekaru 85 a duniya.
Tuni shugabannin kasashen duniya suke aikewa da sakonnin ta’aziyya da tunawa da da irin gagarumar rawar da taka a tarihin isra’ila, haka ma masu sukarsa suma suna bayyana ra’ayoyinsu.

Shugaban Amurka Barack Obama da uwargidansa Michelle sun aike da sakon ta’aziyya ga jama’ gwamnatin Isra’ila da kuma iayalan Mr. Sharon. Sun sake nanata kudurinsu na tabbatar d a tsaron Isra’ila da kuma burin ganin kasashe biyu sun tabbata yankin wadanda suke zaune cikin lumana da tsaro..

Shugaban Isra’ila Shimon Peres wanda ya juma suna abokantaka da mamacin kuma abokin hamayyasa a fagen siyasar Isra’ila, ya kira mamacin da cewa gwarzon a fagen yaki da kuma siyasa, wanda yake kaunar kasarsa, haka ita ma take kaunarsa.

Cikin kalaman farko bayanda aka bada sanarwar rasuwar Mr. Sharon a jiya Asabar a wani asibiti kusa da birnin Tel-Aviv, magajinsa PM Isra’ila na yanzu Benjamin Netantahu ya bayyana bakin cikinsa kan mutuwar Mr. Sharon, daga nan yace har abada Isra’ila ba zata manta da shi ba.

Shugabannin Falasdinu sun yi Alah wadai da Mr. Sharon mutuminda suke adawa shi a duk fadin rayuwarsa. Reshen kungiyar Hamas wacce take rike da Gaza ahalin yanzu, ta kira Mr. Sharon da cewa dan kama karya ne, shi kuma shugaban kungiyar Fatah Jibril Rajoub, ya kira Mr. Sharon da cewa “mai laifi”, ya bayyana bakin jikin ganin ba’a gurfanar da shi gaban kotun kasa da kasa ba.

Babban sakataren MDD Ban ki-moon ya kira Mr. Sharon da cewa jarumi ne a fagen yaki daga bisani kuma ya zama uban kasa dattijo. Ya yabawa Mr. Sharon saboda karfin hali da ya nuna a fagen siyasa a 2005, lokacinda Isra’ila ta janye ‘yan kasarta da kuma sojojinta daga zirin Gaza.