Ana Bincike Kan Yaron Da Aka Daure Tare Da Dabbobi a Kebbi

Hotunan Inda Ake Sayar Da Dabbobi A Jalingo, Jihar Taraba.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi na ci gaba da bincike akan zargin cin zarafi da aka yi wa wani yaro dan kimanin shekara 11 wanda aka daure wuri daya tare da dabbobi har kimanin shekara biyu.

Gwamnatin jihar ta Kebbi dai ta ce ta dauki nauyin kula da lafiyar yaron har yadda hali ya yi.

Lamarin ya faru ne a unguwar Badariya ta garin Birnin Kebbi inda ake tuhumar wani mutum mai suna Aliyu tare da hadin kan matansa uku kan ya daure dansa mai suna Jibril Dan kimanin shekara 11 cikin awaki da talotalo har tsawon kimanin shekara biyu.

Asirin Malam Aliyu da matan nasa ya tonu ne a lokacin da wani mazaunin unguwar ta Badariya ya kyankyasawa wani lauya mai suna Barrister Lagalo wannan batun shi kuma cikin hanzari sai ya sanar da ofishin hukumar kare hakkin dan Adam da ke garin na Birnin Kebbi.

Shugaban hukumar ta kare hakkin dan Adam Hamza Attahiru Wala ya ce daga nan sai suka nemi hadin kan ‘yan sanda suka je gidan domin binciken abinda ke faruwa.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar wannan lamarin kamar yadda kakakin rundunar DSP Nafi'u Abubakar ya sheda wa Muryar Amurka.

Yanzu haka dai kungiyoyin kare hakkin jama'a da dama suna bibiyar wannan batun domin ganin an kwatowa wannan yaron hakkinsa.

Saurari rahoton a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Bincike Kan Yaron Da Aka Daure Tare Da Dabbobi a Kebbi