Kididdiga da hukumar kiyasi ta Najeriya ta fitar ya nuna cewa ya zuwa karshen shekara 2019 ana bin Najeriya bashin kudi daya kai Naira Tiriliyan 4.04 wanda ya yi dai dai da dalar Amurka biliyan 11.17 sannan akwai wasu jihohi da ke da tarin bashi wanda hakan ya taka rawar gani wajen hauhawar bashin Najeriya.
Jihohi irinsu Lagos da Jihar Ribas da Jihar Delta ne ke kan gaba a cikin jerin jihohin da suka fi kowanne yawan bashi a kasar sannan Jihar Yobe ce ke da mafi karancin bashi wanda ya kai Naira miliyan dari bakwai.
Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba yayi nazari inda ya ce akwai wani bincike da yayi a baya inda ya gane cewa akwai wasu kudade na "Stamp Duti" da suka kai Naira biliyan 700 da aka ajiye a babban bankin Najeriya, sannan a shekara 2016 zuwa 2017 ya sake gano wasu kudade har Naira biliyan 600, ya ce ina aka kai kudaden?
Ita kuwa Ministan kudi da tsare tsare Hajiya Zainab Shamsunah Ahmed ta bayyana bashin da ake so a karba a wannan karon ya kai dalar Amurka biliyan 22 da digo 7, wanda za a yi aiyuka da su musamman abubuwan more rayuwa.
Majalisa Dattawa ta ba wasu jihohi, da ma'aikatu, da hukumomin Gwamnati makonni 2 domin su kare wanan kudurin bashin kudi da shugaba Buhari ya nema.
A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5