Ana Amfani Da Kalolin Wuta Wajen Ceto Ran Kananan Yara A Asibiti

Shekaru uku da suka shige ma’aikatan jinya a asibitin gwamnati dake kudancin kasar Malawi suka fara amfani da wani tsari da hukumar lafiya ta duniya ta tsara na tantance kananan yaran da basu da lafiya ta wajen amfani da kalolin wutar bada hanya kan tituna. Ganin yadda ya taimaka wajen ceton rayuka ya sa gwamnatin kasar Malawi ke tunanin fadada amfani da tsarin.

An ceci rayukan kananan yara da dama ta wajen wannan tsarin, domin ana kula dasu kan lokaci a dakunan jinya. Ko da za a turasu wadansu asibitai ma, ana turasu bayan jikinsu ya dan yi sauki a maimakon tura kananan yara da ba tare da an rage zafin ciwon da suke fama da shi ba

Yanzu kananan yara basu mutuwa a layi lokacinda suke jiran jinya. Ba zance ya ragu ba, domin wannan zai nuna har yanzu yana faruwa. Sun daina mutuwa baki daya.

Masu bincike a Malawi suna nazarin nasarar shirin, yayinda jami’ai ke duba yiwuwar amfani da tsarin a wadansu asibitai.