Nigeriya ta na cikin kasashen da 'yan Korea ta arewa suka yi wa bankuna kutse a wuraren da suke yin ajiya a sassa daban daban na duniya.
Baya ga Najeriya sauran kasashen da kutsen ya shafa sun hada da Costa Rica, Ethiopia, Gabon, India, Indonesia, Iraq, Kenya, Malaysia, Poland, Taiwan da Uruguay a cewar kamfanin.
Masana harkokin kudi da tattalin arziki irinsu Dr. Dauda Muhammad Kontagora, a Jami'ar Bayero dake Kano ya na ganin ci gaba da aka samu a fannin yin amfani da kwamfuta ya sa mutum na iya sa kudi a Najeriya ya je Amurka ya fitar da shi.
"Saboda haka idan ba ana yi ana kula da kare kwamfutoci ba tattalin kowace kasa da ta fada hannun masu kutse na iya karyewa." In ji Kontagora.
A cewarsa ya kamata kowace kasa ta dauki matakin gaggawa kamar yadda shi Dr Kontagora ya fada.
Shi dai kamfanin na Kaspersky ya na zargin wani gungun masu kutse da suka yi kaurin suna da ake kira Lazarus da tafka wannan ta'asa.
Sai dai duk da hujjar da yake da ita wacce take nuna cewa adreshin masu kutsen ya samo asali ne daga Korea ta arewa, hakan ba isasshiyar hujja ba ce, domin akwai masu kutse da dama dake gudanar da ayyukansu ba daga inda su ke ba.
A Najeriya ofishin mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro yace a kowace shekara kasar na hasarar miliyan 127 sanadiyar kutse.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5