Dan takarar shugabanci Basalona Augusti Benedito yayi zargin cewa kwamitin gudanarwa na kulab din na kokarin sayar da fitaccen dan wasan ta Lionel Messi.
A halin yanzu shugaban Catalans mai ci yanzu Joseep Maria Bartomeu, ya nuna ra’ayin sa da fatan cewar danwasan gaba na Argentine zai kasance a sansanin Nou zuwa shekru da dama masu zuwa.
Sai dai Benedito cewa yayi sakonnin dake fitowa daga kwamitin gudanarwar Basa ya nuna cewar baza a iya yarda da shi ba.
A wata hira da ya yi ta musamman da mujallar Goal Benedito ya ce “bayanan da suke fitawar a baina jama’a ba dai dai yake da ainihin ra’ayinsu ba.”
Ya kara da cewa a wasu lokuta suna Magana da ta saba yadda suke aiwatar da ayyukansu, ina fata a wannan lamari na Messi ba za a samu haka ba.
##caption:Fitaccen dan wasan gaba na Basalona Lionel Messi.##