An Yiwa ‘Yan Jaridu Bitar Zazzabin Ciwon Sauro a Jihar Gombe

Wadansu kanan yara dake fama da zazzabin malariya

Kwararru a kan harkokin lafiya a Najeriya na ci gaba da nuna fargaba kan matakan da al’umomi a kasar ke daukawa wajen kare kansu daga cutar zazzabin cizon sauro musamman batun tsabtace muhalli da kwanciya cikin gidajen sauro.

Haka ne ya sa hukumar yaki da cutar a jihar Gombe mai samun tallafi daga bankin duniya ta shirya taruruka ga manema labarai da niyar kara masu kaimi wajen fadakar da al’umma a kan muhimmancin kare kai daga cutar.

Dr. Abel Anon babban jami’in hukumar a jihar ya yiwa wakiliyar sashen Hausa Saadatu Mohamed Fawu Karin haske a kan taron.

Your browser doesn’t support HTML5

An Yiwa Yan jaridu bita kan zazzabin malaria - 2:42