An yiwa alkalai bita kan dokokin hadahadar kasuwanci da safarar jirage

Nigeria

Hukumar hadahadar kasuwanci ta jiragen ruwan Najeriya ko kuma Shippers' Council a takaice ta yiwa alkalai bita akan dokokin hadahadar kasuwanci da safarar jirage domin bin ka'idar dokokin kasa da kasa.

An shirwa alakalan bitar ce domin bin dokokin kasa da kasa a lamuran shari'a kan yadda suka shafi dokokin hadahadar kasuwanci da safarar jiragen ruwa

Babban sakataren hukumar Hassan Bello yace irin bitar ga alkalan ta zamo mai mahimmanci domin babu jadawalin koyar da dokokin a makarantu. Bangaren shari'ar da ta shafi kasuwanci da jiragen ruwa a kasa da kasa ake kira Admiralty Law a turance. Wajibi ne alkalan Najeriya su san abun dake faruwa.

Najeriya tana cinikayya da kasashe da yawa ta hanyar hadahadar kasuwanci da jiragen ruwa. Saboda ba'a koyas da dokokin a makarantu ba ya sa hukumar take koyas da alkalan a shirin ko ta kwana. Can baya idan an gabatar da kara da ta jibanci hadahadar kasuwanci da jiragen ruwa sai an dade ba'a cimma hukunci ba. Cinikayya kuma na kasa da kasa baya son hakan.

Kowace shekara aka yi bitar za'a tabbatar Najeriya tana daya da kasashen da suka taso da wadanda ke tasowa domin tabbatar wa wadanda zasu yi hulda da kasar su san tana bin ka'idodi.

Can baya alkalan Najeriya na shan suka kan hukuncinsu da kan ba 'yan Mowa nasara tare da hukumta 'yan Bora.

Shugaban kungiyar yiwa dan Adam adalci Ibrahim Wada Nas yace bitar ta zo daidai lokacin da ake son a yi garambawul a harkokin shari'ar Najeriya. Yace a nashi tunanen kamata ya yi ana yiwa alkalan bita duk wata uku domin yadda suke yanke hukumci nada daurin kai. Wanda ba alkali ba sai ya ga yadda lamari yake amma hukumci ya fita daban. Gaskiya sunanta daya. Idan an gudanar da adalci babu wanda zai yi korafi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An yiwa alkalai bita kan dokokin hadahadar kasuwanci da safarar jirage - 2' 27"