Wadanda suka halarci bukin tarbar dan wasan sun bayyana cewa, banda kasancewarshi dan asalin kasar, dan wasan ya kuma zama gwani a duniya baki daya wanda kasashen nahiyar Afrika baki daya zasu yi alfahari da shi.
Wani mai sharhin a kan lamura ya bayyana cewa, rabon Jamhuriyar Nijar ta sami irin wannan nasarar tun zamanin Isiyaka Dabore, amma gashi yau dan wasan ya daga tutar kasar.
Wani matashi mai wasan barkwanci a Jamhuriyar Nijar, yace wannan nasarar zata karawa matasa karfin guiwa dake sha’awar fitar da sunan kasar a waje. Suka kuma yi kira ga gwamnati su kara bashi goyon baya da kuma dukan ‘yan asalin kasar da suke da basira da kuma gurin yin fice.
A nashi tsokacin, zakaran Taekwondo na Duniya Abdurazak Issoufou Alfaga ya bayyana farin ciki ganin irin tarbar da aka yi mashi da yace zata kara mashi karfin guiwa a wasanni na gaba.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Yusuf Abdullahi ya aiko mana daga birnin Yamai.
Your browser doesn’t support HTML5