An Yi Zanga-Zangar Zaman Lafiya A Filato

  • Ibrahim Garba

Sarkin Jos, Gbong Gwom Jos Jacob Buba Gyang

A wani al’amari na neman jaddada zaman lafiya da cigaba a jahar Filato, kungiyoyin mata na yankin tsakiyar Najeriya sun yin zanga-zangar lumana a harabar Majalisar Dokokin jahar Filato yayin gabatar da kokekokensu don gwamnati ta dau mataki a kai ta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin saboda manoma su samu sukunin nomansu da kuma komawa gidajensu.

Sakataren Yada Labaran Kungiyar Matasan Yankin Tsakiyar Najeriya Arise Clement Selbong y ace dole ne gwamnati ta kuduri aniyar kawo karshen kashe-kashe a yankin. Wata shugabar mata daga Karamar Hukumar Bokkos mai suna Julia John Mangai ta ce akasarin manoma sun rasa muhallansu don haka ya kamata gwamnati ta mayar da su gidajensu.

Kakakin Majalisar Dokokin jahar Filato Peter Azi ya ba su tabbacin cewa Majalisar za ta mika kokensu ga hukumomin da abin ya shafa.

Ga wakiliyarmu Zainab Babaji da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

An Yi Zanga-Zangar Zaman Lafiya A Filato