An Yi Zanga Zanga Kan Kisan Wata 'Yar Rajin Kare Hakkin Bil Adama a Rio de Janeiro

Dubban Mutane Masu Zanga Zanga

A birnin Rio de Janeiro da ke Brazil, an gudanar da zanga zanga domin nuna fushi kan hallaka wata 'yar rajin kare hakkin bil adama da aka yi.

Fiye da mutane 1,000 ne suka yi tattakin jerin gwano daga unguwannin marasa zuwa tsakiyar birnin Rio De Janeiro na kasar Brazil a jiya Lahadi.

An yi zanga zangar ce don nuna takaicin kisan wata mace ‘yar rajin kare hakkin bil’adama Marielle Franco da aka yi.

Masu shirya zanga zangar sun yi amfani da na’urorin daukaka amon sauti suna cewa, muryarta ba za ta yi shiru ba a lokacin da zanga zangar ta kai har kan babban layin garin.

An harbe Franco da direban ta a ranar Larabar da ta gabata yayin da suke barin wani taro da aka yi na goyon bayan bakaken mata.

Franco tana cikin ‘yan majalisar gudanar da harakokin raya birnin Rio de Janeiro kuma ‘yar rajin kare ‘yancin ‘yan tsiraru ce.

Ta kan yi magana akan yadda 'yan sanda muzgunawa jama’ar da ke zaune a unguwannin marasa galihu.