An Yi Yunkurin Juyin Mulki a Haiti

Hukumomi a Haiti sun ce sun dakile wani yunkurin da aka yin a kashe shugaba Jovenel Moise tare da kifar da gwamnatinsa a jiya Lahadi, yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan yaushe wa’adin mulkinsa zai kare.

”Harin na juyin Mulki ne” a cewar Ministan shari’a Rockefeller Vincent, mahukuntan sun kara da cewar kimanin mutum 23 aka kama, da suka hada da wani babban Alkali da wani jami’in ‘yan sanda.

”Ina godiya ga shugaban jami’an tsaro fadata. Burin waddanan mutane shi ne su kashe ni, Amma burinsu bai cika ba, a cewar Moise. ”

”Shugaban Moise dai na jagorantar kasar ba tare da an bincike shi ba, kuma ya ayyana cewa zai ci gaba da zama a karagar mulki har zuwa ranar 7 ga watan Fabrairiun 2022

kamar yadda ya fassara kundin tsarin mulkin kasar, wanda ‘yan adawa suka ki amincewa, lamarin da ya haddasa zanga zangar neman ya sauka a mulki a ranar Lahadi.