An Yi Waje Da Golden Eaglets Ta Najeriya A Gasar Kopin Duniya Na U-17

Golden Eaglets, 'yan wasan Nigeriya 'yan kasa da shekaru 17

Zakarun Najeriya kasa da shekaru 17 sun yi waje a gasar cin kopin duniya a kasar Brazil, bayan sun sha kashi da ci uku da daya a hannun Netherlands da safiyar jiya Laraba.

Dan wasan gaba Netherlands Sontie Hansen, shine ya zura kwallaye ukun, lamarin da ya kawo karshen Golden Eaglets ta Najeriya a cikin gasar ta duniya.

Dan wasan na Ajax ya fara zura kwallaye biyu ne da fara wasan da mintuna 15 inda kungiyarsa ta Netherlands ta shige gaba a wasan kana ya zura kwallon karshe ta bugu panaliti a lokacin da wasan ya kai mintuna 80.

Sakamakon wannan wasa na nufin kasar ta Dutch zata hadu da wanda zai yi nasara tsakanin Paraguay da Argentina a wasan kwata final, yayin da Golden Eaglets ta Najeriya da ta lashe wannan kopin na duniya sau biyar ta kama hanya zuwa gida.

Golden Eaglets dai sun sha fama kafin suka lashe wasanni biyun karshe na matsayin rukuni kafin tayi fice zuwa ga matsayi na gaba.

‘Yan wasan Eaglets da Manu Garba ke horar dasu basu iya kai labari ba a wasannin matsayin na “Round 16”