WASHINGTON, D.C —
Hukumomi a birnin Wuhan na kasar China, sun ce sun yi ma ilahirin mutanen birnin gwajin cutar COVID-19, wanda hakan na daya daga cikin matakan da kasar ke dauka na maido da kwarin gwiwar ‘yan kasa, da kuma harkokin tattalin arziki.
Wannan gagarumin gwajin da aka yi, ya nuna cewa mutane 206 ne kadai ke dauke da cutar ta COVID-19, wadanda kuma dukkansu ke rukunin gyauron cuta.
Tun bayan barkewar cutar zuwa yanzu, birnin ya ba da rahoton kamuwar mutum sama da 50,000 da cutar.
Masu lura da al’amura na ganin an gudanar da gwajin ga mazauna yankin ne saboda a karfafa ma jama’a gwiwa, fiye da zama wani matakin kiwon lafiya.
Wuhan ne dai birnin da cutar ta fara bulla a karshen watan Disamba.