Gwamnatin jahar Logas ta kafa wata doka ta haramta tallace-tallace a birnin Lagos mai cike da hada-hadar kasuwanci, wanda saboda haka kuma ya ke janyo jama’a sosai ciki har da ‘yan arewacin Najeriya, wadanda da yawansu ke kasuwanci har da na talla a gefen hanya , al’amarin da gwamnatin jahar ta Lagos ke cewa na haddasa matsala ga matafiya da kuma yin barazana ga tsaron lafiyar jama’a da dai sauransu.
To amma wasu masu gudanar da irin wadannan sana’o’i na talla kan titin Lagos da makamantansu, sun shaida ma wakilinmu a Lagos, Babangida Jibrin cewa haka ya tauye masu hakkinsu na ‘yan kasa da kuma nayoyin samun abin zaman gari. Wani mai suna Abdullahi y ace sun je Lagos ne don gudanar da sana’o’in cewar da iyalansu. Don haka muddun aka aiwatar da wannan dokar, to ba a kyauta masu ba ko kankani. Y ace ya kamata a yi la’akari da cewa gari fa sai da baki yak e cigaba, muddan baki su ka bar gari to gari ya lalace.
To saidai Babangida y ace a gefe guda kuwa, gwamnatin jahar ta Lagos ta dage cewa matakin da ta dauka zai taimaka wajen kawar da zauna gari banza da kuma matsalar tsaro. Hasali ma gwamnatin ta fara kama masu irin wannan tallace-tallacen. Wani daga cikin wadanda aka taba kamawa mai suna Tahiru daga jahar Sakkwato, ya bayyana cewa an ci shi tarar Naira dubu goma sha biyar, baya ga kwace masa kaya da aka yi. To saidai wani jami’in gwamnatin ta Lagos, wanda bai son a bayyana sunansa, ya ce akasarin wadanda aka kama din kananan yara ne, wadanda bai ma kamata a barsu su rinka yawo bisa titi ba.
Your browser doesn’t support HTML5