An bayyana yadda harkar ilimi ta durkushe a Nijeriya da cewa wani abin bakin ciki ne da kunya ga kasa irin Nijeriya.
WASHINGTON —
An bayyana yadda harkar ilimi ta durkushe a Nijeriya da cewa wani abin bakin ciki ne da kunya ga kasa irin Nijeriya.
Da ya ke bayyana ra’ayinsa game da yajin aikin malaman jami’o’in Nijeriya da kuma barazanar korinsu da gwamnati ta yi, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum mai suna malam Kabiru Danladi Lawanti na Sashin Ilimin Koyar da Aikin Jarida Na Jami’ar Ahmadu Bello Ta Zariya (ABU), ya ce duk wannan bai taso ba. Ya ce abin takaici ne ace wai a irin halin da ake ciki a Nijeriya gwamnati za ta fito ta ce wai za ta kori malaman Jami’a. Malam Lawanti ya ce dama jami’o’in kasar na bukatar karin malamai akalla dubu sittin, sannan kuma ace wai za a kori malaman, wadanda dama ake fama da karancinsu ai ba fa’ida cikin wannan shawarar.
Malam Lawanti ya yi nuni da cewa sai fa an yi akalla shekaru 15 kafin a horar da malami ya zama furfesa. Ya ce sai idan an yi sa’ar samun mutun mai tsabar hazaka kafin a iya horar da shi ya zama furfesa cikin shekaru 7, sannan kwatsam a ce wai za a kori malaman jami’a ai wannan bai dace ba. Kodayake malamin ya ce ba yau aka fara irin wannan barazanar ba. Ya ce akwai gwamnatin da ta taba yin hakan amma kuma daga baya ta dawo da malaman.
Malamin ya ce da ace Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya mai da martani ga wasika da kungiyar ASUU ta aike masa ran 25 ga wata da ba a kai ga haka ba; hasalima da an janye yajin aikin. Ya ce tun kafin Shugaban Kasa ya mai da martani kawai sai aka ji Ministan Yada Labarai na fadi ta kafar yada labarai cewa malaman Jami’a su koma bakin aiki ko a kore su. Y a ce wajen kashi 90% na jami’o’in Nijeriya sun yadda a koma bakin aiki in banda wasu ‘yan sharudda kamar guda uku da su ka gindaya.

Your browser doesn’t support HTML5