An Yi Taron Yaki Da Cutar Malaria A Lagos

Malaria

A taron masu hada magunguna da aka yi a Lagos, gwamnatin tarayya ta kira hadin kai da kamfanonin magunguna da gwamnatin a wani yunkurin shawo kan cutar malaria wadda take kashe kimanin mutane dubu dari uku a Najeriya kowace shekara

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kira kamfanoni dake hada magunguna masu zaman kansu da su hada hannu da gwamnatin domin yaki da cutar malaria.

Karamin ministan kiwon lafiya Dr. Osagie Ehemire shi ya yi kiran a wajen wani taro da aka yi tare da kamfanoni masu zaman kansu a kokarin da ake yin a kawo karshen cutar malaria a Afirka.

Taron an gudanar dashi ne a karkashin wata kungiya mai suna Corporate Alliance On Malaria In Affrica, an shirya sh ne domin tattauna matakan da za’a dauka akan cutar ta malaria.

Ahmad Yakasai shi ne shugaban kungiyar masu hada magunguna ta Najeriya ya bayyana matakan da suke dauka na yaki da malaria.

Cikin matakan da suka dauka shi ne kafa cibiyar binciken magungunan gargajiya da kasar ke dasu har ma sun gano magunguna guda takwas da suka hada da maganin warkar da nakasar kwayoyin jini. Shi maganin ya samu karbuwa har ma a kasashen waje. Akwai maganin malaria da mai ba masu cutar kanjamau karfin jiki.

Kawo yanzu bincke ya nuna mutane dubu dari uku ne cutar malaria ke hallakawa a Najeriya kowace shekara baicin sauran kasashen Afirka.

Gwamnati na ganin hada kai da kamfanonin dake hada magunguna zai taimaka wajen yaki da cutar a nahiyar Afirka baki daya.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

An Yi Taron Yaki Da Cutar Malaria A Lagos - 3' 26"