An Yi Taron Wayar Da Kan Jama'a Akan Zabe a Jihar Borno

Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Borno, Alhaji Ibrahim Magaji ya yi bayani akan zabukan da za a gudanar a jihar. Yace akwai kananan hukumomi guda 8 cikin 27 da ake da su a jihar da za a gudanar da zabe a sansanonin ‘yan gudun hijira da aka yiwa rijistar kuri’u dubu dari hudu da tara da dari takwas da talatin da uku. Da suka hada da karamar hukumar Kalabalge, da Marte, Dukkwa, Ngala, da Kukawa da sauran su.

Alhaji Magaji ya yi wannan bayanin ne a wani taron masu ruwa da tsaki akan harkokin zabe da kungiyar ‘yan jarida reshen jihar Borno ta kira, don wayar da kan jama’a akan zaben da ake shirin yi.

Kwamishinan hukumar zaben jihar ya ce ya zuwa yanzu dai basu da wata matsala, kusan duk abinda suke nema sun samu. Ya kuma ce a halin yanzu akwai katunan din-din-din kusan dubu dari da ba a karba ba.

Alhaji Yahaya Imam, shugaban hukumar wayar da kan jama’a na kasa, reshen jihar Borno, ya ce batun sayar da kati na daya daga cikin abubuwan da suka fi maida hankali akai wajen wayar da kan jama’a. Ya kuma kara bayyana illar sayarda katin zaben.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Yi Taron Wayar Da Kan Jama'a Akan Zabe a Jihar Borno - 3'43"