An yi taron amincewa ko rashin amincewa da ayyukan da gwamnatin jihar Gombe tayi a karkashin shugabancin gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo.
Bayan taron wasu da suka halarci taron sun fadi albarkacin bakinsu.Wata tace tsarin da gwamnan ya fito dashi ya gama komi. Ya nuna halin dattaku, shugabanci mai adalci da kuma son cigaban jihar ba domin kansa ba sai dai domin cigaban jihar.
Onarebul Abubakar Muhammad magajin garin Kwadam ya gode da aikin da aka yi saidai yace ba'a san wadanda ke yin kwangilolin ba. Tana yiwuwa 'yan kwangilar ma su manta da aikin kwangilar nan gaba. Yace a gayawa gwamna akwai 'yan kwangila da zasu yi watsi da ayyukan da aka basu.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Yariyo Jonh Lazarus dan Jarman Waja yace idan an dubi ayyukan da gwamnan yayi bai kamata ma a ce wani yana hamayya dashi ba. Ayyukan da yayi cikin shekaru hudun nan ba'a yi irinsu ba cikin shekaru takwas na gwamnatin da ta shude ba, wato ayyukan da Dankwambo yayi sun fi nasu.
Ambassador Abdulmunmuni Abubakar tsohon babban sifeton 'yansandan Najeriya yace tunda aka kafa jihar a shekarar 1996 babu wani gwamna da yayi ayyukan da suka taba rayukan jama'a kamar na Dankwambo.
Ado Solomon na hukumar wayar da kawunan jama'a dake Abuja yace taron da gwamnan ya shirya abu ne da yakamata kowace jiha tayi koyi dashi domin mutane su san gwamnati tasu ce.
Shi ma gwamnan Ibrahim Dankwambo ya jaddada mahimmancin taron. Ya mika godiyarsa ga jama'a kana ya gargadesu su zauna lafiya
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5