Bill Gates Da Dangote Da Jihohin Arewa Shida Suna Yiwa Cutar Polio Taron Dangi.

Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

Manyan attajiran duniya biyu da gwamnoni shida na arewacin Najeriya da sarakunan gargajiya da manyan ma'aikatan kiwon lafiya suka halarci taron shawo kan cutar polio a Sokoto tare da rabtaba hannu akan yarjejeniyar da aka cimma da gidauniyar Bill and Melinda Gates da ta Dangote

An yi taron masu ruwa da tsaki da suka hada da manyan attajiran duniya Bill Gate da Aliko Dangote, da gwamnonin jihohin Sokoto, Kano, Kaduna, Bauchi, Borno da Yobe.

Kazalika sarakunan gargajiya a karkashin jagoranci Sarkin Musulmi Muhamamad Sa'ad Abubakar III da Ministan kiwon lafiya ma ya kasance a taron da sugabannin hukumomin kiwon lafiya matakin farko na Najeriya tare da manufar hada karfi da karfe domin dakile cutar shan inna ko polio.

Taron ya samar da yarjejeniyar yin aik tare wadda aka rabtabawa hannu tsakanin gwamnatoci da tallafin attajiran da sauran hukumomin bada tallafi na kasa da kasa.

Shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, Bill Gates ya sha alwashin ci gaba da bada tallafi to amma ya bukaci a hada karfi da karfe wurin yin aiki tare.

Aliko Dangote shi ma ya yi alkawarin bada tallafi a karkshin tashi gidauniyar tare da bada shawara. Ya ce akwai bukatar daukan matakan gaggawa domin shawo kan cutar polio da sauran cututukan da suka addabi jihohin arewa.

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce jiharsa ce tafi cin gajiyar tallafin gidauniyoyin Bill da Melinda Gate da Dangote ta fannin kiwon lafiya da majalisar Sarkin Musulmi.

Shi ko gwamnan Borno Kashim Shettima ya ce kodayake sun samu matsaloli saboda rikicin Boko Haram har yanzu akwai wuraren da basu iya shiga ba amma an samu ci gaba.

Duk gwamnonin shida sun rabtaba hannu akan yarjejeniyar da suka cimma.

A saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

An Yi Taron Shawo Kan Cutar Polio A Sokoto - 2' 49"