An gudanar da taron fadakar da jama'a akan yunkurin gwamnatin tarayyar Najeriya na kirkiro kasuwar Afirka ta bai daya da za'a kira African Continental Free Trade Area a turance.
Kasuwar zata ba 'yan Afirka damar gudanar da harkokin kasuwancinsu cikin sauki.
An gudanar da taron ne a garin Maidugri dake jihar Borno, jihar dake makwaftaka da kasashen Afirka uku, wato Nijar da Kamaru da Chadi.
Tawagar dake taron fadakar da kawunan jama'a tana zagaya jihohin kasar ne game da muhimmancin kafa kasuwar.
Chinedu Osakwe wanda ya jagoranci tawagar dake fadakar da kawunan jama'a ya ce ana son a gina kasuwar ne a arewa maso gabashin Najeriya da zummar habaka kasuwanci tsakanin Najeriya da kasashen Afirka ta Tsakiya zuwa kasashen dake gabashin Afirka. Kasuwar zata taimakawa 'yan kasuwan Najeriya fitar da hajojinsu cikin sauki tun daga arewa maso gabashin kasar zuwa kasashen Afirka ta yamma har zuwa sauran kasashen nahiyar.
A ganin Chinedu Osakwe, ya kamata bankunan masana'antu su samar ma 'yan kasuwan Najeriya rancen jari da gudummawa ga kanana da manyan masana'antu. A cewarsa abun kunya ne a ce kashi 17 na kasuwancin Afirka yake wakana da kasashen Afirka. Duk sauran suna na yi ne da kasashen waje. Amma idan an samar da kasuwar Afirka ta bai daya lamarin zai canza.
Injiniya Awal Ibrahim, shi ne mataimakin shugaban kanana da matsakaitan masana'antun Najeriya, ya ce kafa kasuwar wani yunkuri ne na hana kasuwannin bayan fage domin a tabbata kudin na shiga kasar ta hanyar da ta dace kamar yadda kudin man fetur ke shigowa kasar.
Alhaji Audu Umar shugaban kungiyar Unity Forum, wata kungiyar kasuwanci ya ce kafa kasuwar zata basu damar zuwa wasu kasashe su sayar da kayansu wasu kuma daga kasashen Afirkan na iya shigowa kasar su sayi kayansu.
Sardaunan Damaturu Alhaji Arabi Ahmed Bello,ana nasa jawabin yace idan sun fahimta, yadda dai kasuwar Turai take, haka ake son a yi ta Afirka wanda ya nuna akwai dan alfanu amma suna da tambaya akan yadda wannan al'amari zai kusanci karamin dan kasuwa da talaka.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5