An Yi Taron Duba Na Mabiya Addinin Gargajiya A Nijar

  • Ibrahim Garba

Shugaban Nijar Issufu Muhammadu

Yayin da bangarori daban-daban a Janhuriyar Nijar ke ba da gudun mowarsu kan yadda za a ciyar da kasa gaba, su ma mabiya addinin gargajiya sun yi taro inda su ka bayar da tasu gudunmowar.

Yau a Janhuriyar Nijar an yi taron duba na shekara-shekara na mabiya addinin gargajiya, inda ‘yan bori da sauran masu duba su ka yi ta dube-dube da bayanin abubuwan da su ka ji daga alhanunsu.

Wakilinmu a Yamai Souley Mamman Barma y ace mabiya addinin gargajiyar kasar “kan gudanar da taronsu na shekara shekara wato budin daji domin hango yadda shekarar za ta kasance a wannan kasa domin daukar matakan kare jama’a daga duk wani bala’in da aljannu suka sanar.

Mataimakin Sarkin Borin Yamai Mamman Garba ya ce aljannu sukan gaya masu irin dabbobin da su ke bukata a yanka don su bayyna masu abubuwan da za su faru a kowace shekara. Yace sukan bayyana masu ko za a samu ruwa ko hatsi a shekarar ko babu.

Sarkin Bori Seini Sule Bankano ya ce bayan bincike na tsawon mako guda aljanun sun gaya masu abubuwan da za su faru a wannan shekarar. Y ace an shaida masu cewa damanar bana babu laifi. To saidai sun koka kan kyamar da su ka ce ana nuna masu.

Ga dai wakilinmu Souley Mummuni barama da cikkken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

An Yi Taron Duba Na Mabiya Addinin Gargajiya A Nijar - 2'41''