Taron yayi kokarin gano bakin zaren banbance banbance da kowane bangaren kasar ke ikirari domin a zauna lafiya.
Farfasa Anya O. Anya daga jihar Abia shi ya fara shimfida a wajen tattaunawar. Yana mai cewa a duba banbance banbancen al'adunmu wadanda "idan aka yi la'akari dasu ka iya zama madaurinmu da zasu karfafa zamantakewarmu". Ya cigaba da cewa "idan an yi la'akari da yadda matasan kasar daga sassa daban daban ke yin tawaye dole ne dattawan kasar su tashi su shawo kansu domin a cigaba da zama kasa daya dunkulalla".
Tsohon ministan labarai Farfasa Jerry Gana yana ganin sai an sake fasalin kasar tukun. Yana mai cewa "a kowace kasa dake da banbancin addini, al'adu, harsuna, dabi'u da dai sauransu gwamnatin tarayya a keyi yadda akwai abubuwan da jihohi zasu yi kana akwai na jihohi". Yace "amma a shirin Najeriya komi ya taru a hannun gwamnatin tarayya ne. Komi za'a yi sai an tunkari Abuja. Bai kamata a yi haka ba. Ana mulki kaman na soja wanda lokacinsu komi na hannun gwamnatin tarayya. Idan ana son zaman lafiya, jihohi a basu isasshen aiki da zasu yiwa mutanensu. Idan an yi hakan mutane ba zasu damu da Abuja ba".
Shi kuwa Injiniya Buba Galadima yana ganin ana "yamutsa addini da siyasa da kuma son zuciya a harkokin kasar". Ya bada shawara yana cewa "babbar matsalar da ta shafi kowa ita ce katsalandan da shugabannin addinai su keyi kamar suna gasa da juna. Sun manta hanyoyin addini sun koma kan siyasa". Yace "Muddun bamu kawar da irin wadannnan daga cikin halayenmu ba Najeriya ba zata taba cigaba ba".
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5