An Yi Taro Kan Dokar Kula da Hakkin 'Yan Gudun Hijira A Yola

Taron wayar da kawunan 'yan jarida a Yola

Kungiyar dake kula da harkokin majalisu, CISLAC, da hukumar dake kula da 'yan gudun hijira, UNHCR, ta Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Switzerland suka shirya taron fadakar da 'yan jarida da wasu akan hakkin 'yan gudun hijira a Yola babban birnin jihar Adamawa

Yayin dai wannan taron tuntuba da cibiyar sa ido kan harkokin majalisu, CISLAC tare da hadin gwuiwar hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya,UNHCR da kuma ofishin jakadancin kasar Switzerland suka shirya ,an gayyato wakilan kafofin yada labarai daban daban da sauran masu ruwa da tsaki da zummar duba hanyoyin tabbatar da dokar kula da hakkokin yan gudun hijira.

Haka nan mahalarta taron sun yi dubi game da matsalolin rashin samun cikakkun bayanai daga hukumomin da nauyin kula da yan gudun hijira ya rataya a wuyansu,musamman idan ya shafi badakala,ko kuma cin zarafi.

Mr Okeke Anya dake zama daraktan sha’anin harkokin gwamnati na cibiyar ta CISLAC, ya ce rashin samar da dokoki,da kuma bayanai na cikin matsalolin dake hana ruwa gudu,na magance wasu matsalolin da yan gudun hijira ke fuskanta.

‘’ Wannan nauyi ne da ya rataya akan kungiyoyi da ku yan jarida domin tabbatar da dokar da kuma sanin halin da ‘yan gudun hijira ke ciki.Dole a hada hannu don haka ta cimma ruwa!

Ya zuwa yanzu dai tuni aka kafa dokar samun bayanai ta Freedom of Information,to amma kuma duk da wannan doka ba kasafai kwalliya kan biya kudin sabulu ba.To ko me kungiyar yan jarida zata yi musamman kan batutuwan da suka jibanci ‘yan gudun hijira? Mallam Umar Dankano,mataimakin shugaban kungiyar yan jarida ta NUJ a jihar Adamawa na cikin mahalarta taron ya ce, zasu tashi tsaye.

Cibiyoyin kiwon lafiya,suma akwai rawar da ya kamata suna takawa wajen tallafawa ‘yan gudun hijira.To ko anya suna yi kuwa? Mallam Adamu Dodo jami’in hulda da jama’a ne na asibitin gwamnatin tarayya dake Yola,wato FMC, ya bayyana irin kokarin da suke yi.

Yanzu haka baya ga rikicin Boko Haram wata matsalar dake jawo yawaitar ‘yan gudun hijira a Najeriya ita ce ta tashe tashen hankulan da ake fama dasu a yanzu,batun da mahukunta ke cewa suna nasu kokari.