Daya daga cikin jigajigan daraktocin fina-finai kuma dan kungiyar MOPPAN, dake kula da farfajiyar finafinan Hausa wadda aka fi sani da Kannywood Malam Falalu Dorayi, ya bayyanawa dandalinvoa cewar an yi sulhu akan takaddamar data shiga tsakanin wasu daga cikin fitattun jaruman Kanywood biyu da suka bawa hammata iska.
Da yake jawabi, Dorayi ya bayyana cewa an sasanta tsakanin jaruman su biyu, Hadiza Gabon, da Nafisa Abdullahi, a gaban wasu mutane guda bakwai, hudu daga Kannywood, sauran ukun kuma jami'an 'yan sanda ne.
Falalu, ya kara da cewa jama'a su guji kama jita-jita domin a cewarsa magulmata na iya shiga tsakanin aminai ta hanyar yada kananan maganganu da ka iya haifar da matsala a zamantakewa.
Domin karin bayani, saurari hirar a nan.
Your browser doesn’t support HTML5