Kasar Iran da Amurka sun yi wata musanya mai wahala ta sakin fursunonin juna a yau Asabar. Inda suka amince a gaban jami’an diflomasiyyar da suka taru a Vienna don karkare maganar takunkuman dake harde da Iran.
Cikin wadanda aka saki din har da Ba’amurken dan jaridar nan Jason Rezaian na Jaridar Washington Post, Sai wani Fasto, da wani sojan ruwa Ba’amurke dan asalin Iran. Gaba daya Amurkawan guda 5 aka saki.
Su kuma Amurka za su saki wasu Iraniyawa guda 7 da aka tsare kan zargin karya ka’idojin takunkuman karya tattalin arzikin Iran, da kuma wasu da ake tuhuma suma duk za a sake su.
Amurka ta bada sanarwar cewa ta yafewa dukkan wadanda ake zargin, kama tun daga kan wadanda ke tsare a gidan wakafi da kuma wadanda ake kan shari'arsu. An dai kwashe watanni 14 ana muzurai kafin kafin a cimma matsaya.