Gwamnatin jahar Kaduna ta tabbatar da kisan gillar da wasu miyagun da ba a san ko su waye ba, su ka yi ma Mai Martaba Sarkin Numana, Malam Gambo Makama da matarsa a gidansu da ke masarautar ta Numana a karamar Hukumar Sanga da ke jahar Kaduna.
Daraktan yada labaran gwamnatin jahar Kaduna Mr Samuel Aruwan ya ce gwamnatin jahar ta samu bayanai daga jami’an tsaro da kuma sauran majiyoyi sahihai cewa lallai wasu mutanen da har yanzu ba a tantance ko su waye ba, sun hallaka Sarkin na Numana da matarsa a gidansu a Karamar Hukumar Sanga. Mr. Aruwan ya ce gwamnatin jahar ta yi tir da wannan aika-aikar, kuma ta sha alwashin farauto makasan sarkin. Ya ce gwamnati na kiran jama’a da su kai zuciya nesa.
Mr Aruwan ya kuma ce tuni gwamnati ta tura jami’an tsaro a yankin don kare rayuka da kuma dukiyoyin jama’a. Ya ce a maimakon a tayar da jijiyoyin wuya kamata ya yi a tuntubi masu bincike da kuma sauran hukumomin da ya dace muddun ana da wata kwakkwarar shaida ko wani bayani. Ga Isa Lawal Ikara da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5