Kungiyoyin matasa a jihar Platon Nigeria sun dukufa wajen fadakar da junansu illar dake tattare da tashin hankali a lokacin zabe.
Daya daga cikin irin wannan kungiyoyi, itace kungiyar matasa mai suna Plateau Youth For Peace, wadda ta dukufa wajen wayar da kan matasa da cewa rayuwarsu ta fi muhimmanci fiye da zabe, a saboda haka basu ga dalilin da matasa zasu sadaukar da ran su saboda wani dan takara ba.
Yakubu C. Gam shine shugaban wannan kungiya. Yace babu abinda yafi ran su, kuma babu abinda yafi musu mutunci tsakaninsu da junansu. Yace kada jam'iyar PDP ta zama dalilin da matashi daya zai rasa ransa. PDP kada ta zama dalilin da zai sa wani addini yafi wani. Domin kuwa yace idan aka samu damuwa, yara da mata sune sua fi tagaiyara. Haka suma matasa suna shiga halin wahala. Kazalika wadanda basu san hawa ba basu san sauka ba, suma suna wahala. Bayan an gama zabe sai a bar su da takaici ko kuma dana sani.
Shima Sakataren kungiyar Lawal Bala, yace sun yiwa matasa hudubar cewa kada su yadda lokacin zabe ana zuwa gidajen sayar da giya ana saye a baiwa matasa su sha su fita hayacinsu. Ko kuma kwaya da wiwi da sauran su da zasu sa matasa shiga cikin maye, don ayi amfani dasu wajen kawo rikici a wuraren zabe.
Bugu da kari tashin hankali na shafar dukkan bangarorin rayuwa.
Your browser doesn’t support HTML5