An kira masu hannu da shuni a Najeriya da su yi koyi da Alhaji Aliko Dangote saboda da yawan taimako da ya ke yiwa al'umma, kungiyoyi da ma gwamnati.
A baya bayan nan hamshakin attajirin ya ba da tallafin motoci dari da hamsin wa 'yan sandan Najeriya domin inganta matakan tsaro a kasar.
Mai martaba sarkin hausawan Enugu Alhaji Yusuf Sambo shi ya kira attajiran kasar da su yi koyi da Alhaji Aliko Dangote a wata hira da ya yi da Muryar Amurka.
Ya ce abin da Dangote ya yi na tallafa wa 'yan sandan Najeriya abin da ake so ke nan daga wajen attajirai saboda tsaro ke kawo zaman lafiya da ci gaba a kasa. Irin abin dake faruwa a Zamfara da Kaduna da sauran wuraren abin tashin hankali ne.
Shi ma Alhaji Abudullahi Yaya Biu ya yaba da taimakon da Dangote ya bayar tare da cewa motocin zasu taimaka da fatan sauran masu hali a kasar zasu taimaka.
Amma wani malamin dake koyaswa a wata makarantar sakandare a garin Owerri ya ce lallai 'yan Najeriya sun anfana da kyautarsa kamata ya yi kasar ta gode masa.
Malam Abdullahi Baban Hadiza Rigasa wani mai sharhi akan lamuran yau da kullum yana ganin da jami'an tsaron aka yiwa kyautar domin zasu fi samun karfafawa da kara hazakar aiki
A saurari rahoton Alphonsus Okoroigwe da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5