An Yi Kira Ga Al'ummomin Adamawa Da Taraba Da Su Fito Sosai A Zabukan Gaba

  • Ibrahim Garba

Jami'an INEC na tantance kayan zabe

Yayin da zabukan gwamnoni da 'yan Majalisun Jihohi ke kara karatowa, an yi kira ga al'ummomin jihohin Adamawa da Taraba da su fito sosai don zabar nagargaru.

An yi kira ga al’ummomin jihohin Adamawa da Taraba da su fito kwansu da kwarkwatansu su kada kuri’unsu fiye da yadda su ka yi a baya. Wannan kiran ya biyo bayan rashin fitowa sosai da masu kada kuri’a su ka yi a wadannan jihohin.

Wakilinmu a jihar Taraba Ibrahim Abdul’aziz, ya ruwaito wani shugaban addini, Dr. Ibrahim Jallon a cewa matakar dai mutanen Taraba na son cigaba, to sai fa sun fito sun zabi mutanen da su ka cancanta. Don haka y ace wajibi ne a zabi adilai da kuma wadanda ke tare da adilai. Ya ce gayyar adilai kan rinjayi tsirarun cikinsu. Don haka akwai bukatar a yi la’akari da inda ake da tarin nagargarun mutane a zabe su saboda za su iya canza alkiblar miyagun cikinsu marasa rinjaye.

Su ma Fulani makiyaya sun yi kiran da a kara azama wurin ganin cewa an zabi wadanda su ka dace. Wani Shugaban Fulani, Hardo Ibrahim Mutunbiyu, ya yi kira ga Fulanin jihar Taraba da su fito ranar Asabar kwansu da kwarkwatansu su kada kuri’a sosai, su zabi abin da zai fi zama alheri ga jama’a.

Su ma wasu daga cikin ‘yan takarar gwamnan sun yi kira. Wani na kusa da ‘yar takarar gwamna ta jam’iyyar APC mai suna Malam Salisu Bawa ya ce ‘yar takarar ta su, Hajiya A’ishatu Jummai Alhassan, saboda, a cewarsa, itace kawai za ta iya hada kawunan mutane ganin yadda aka rarraba kawunan mutane ta hanyar addini da kabilanci da sauran dabaru. To saidai su kuma ‘yan PDP irinsu Alhaji Hassan Karofi su na ganin dan takararsu Mr. Darel Ishaku shi ne zai lashe zaben saboda, a cewarsa, ko lokacin zaben Shugaban kasa da na ‘yan Majalisun Tarayya, jam’iyyarsu ta PDP ce ta yi galaba a jihar Taraba.

Your browser doesn’t support HTML5

ADAMAWA, TARABA, APC, PDP 3'51''