Kafafen yada labarai da dama sun ruwaito cewa Osinachi Nwachukwu wacce aka fi sani da wakarta “Ekwueme” ta rasu ne a watan Afrilun da ya gabata sakamakon bakar azabar da ta sha daga hannun mijinta Mista Peter Nwachukwu, wanda ya ke fuskantar shari’a a babban birnin tarayyar Najeriya na Abuja.
Da ta ke jawabinta a wurin jana’izar, Honarabul Nkeiruka Onyejeocha da ke wakiltar Isuikwuato/Umunneochi a majalisar wakilai ta tarayya, ta bayyana takaici kan abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mawakiyar.
Ta ce, “Abin takaici ne cewa ‘yar’uwan mu ta wuce . Kuma abin takaici ne cewa ta mutu. Da kuwa mun so ta rayu. Kuma ga wacce ta sadaukar da ranta ga Allah tana rera wakoki, ba abin da ya rage mu yi illa mu rera wakoki har karshen jana’izarta. Yanzu matukar muna so kasar nan ta rayu, dole ne mu koma ga Allah, saboda shi kadai ne ya isa ya cece mu daga halin da muka tsinci kan mu a ciki.”
Honarabul Nkeiruka Onyejeocha dai ta karkare da yin alkawarin daukar nauyin horar da ‘ya’yan marigayiyar har matakin jami’a.
An gudanar da jana’izar ne a wani yanayi mai cike da wake-wake na addinin Krista, inda mutane da yawa, musamman mawakan bishara, su ka yi tsokaci game da irin kyakkyawar rayuwar da marigayiyar ta yi a lokacin da tana raye.
Ku Duba Wannan Ma Kannywood Na Jimamin Rasuwar Ahmad TageFasto Dan Orji ya ce, “Osinachi ta kasance Krista har zuwa matakin da mutane zasu so su kwaikwayi tafarkin rayuwar ta. Osinachi Krista ce ta kwarai, kuma a nawa ganin ta gama da duniya lafiya.”
Ita kuwa Promise Miracle ta dubi salon wakarta, kuma tana ganin an anfana sosai da wakokinta.
Ta ce, “Duk lokacin da ta ke waka, zaka ga ni’imar zuciyarta, da kuma dangantakarta da Allah. Osinachi mace ce mai tsoron Allah, kuma ta dauki sana’arta da muhimmanci. Saboda haka, mun zo nan ne mu gode wa Allah akan rayuwarta.”
Osinachi wacce ta rasu tana da shekaru 42 a duniya, ta bar ‘ya’ya hudu, da ‘yan’uwa, da kuma dangi da yawa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5