An yi jana'izar sama da mutum 30 da suka rasa rayukansu bsanadiyyar wani hari da 'yan bindiga suka kai a yankin Shinkafi da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya a karshen makon da ya gabata.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta tabbatar da aukuwar harin, inda ta ce tana daukar matakan dakile ayyukan ‘yan bindiga a jihar, kamar yadda SP Muhammad Shehu ya bayyana.
Wannan harin ya biyo ne sa’o’i kalilan, bayan da sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar ya fitar da sanarwarsa ta farko, inda ya sha alwashin ganin bayan mahara da masu satar mutane domin neman kudin fansa.
Amma ya ce zai ba da karfi wajen kokarin sasantawa da afuwa ga ‘yan bindigar da ke bukatar hakan.
Sai dai kuma jama’ar yankunan da ke fama da hare-haren na tababar tasirin wannan matakin, lura dacewa irin wannan yunkuri a can baya bai yi tasiri ba.
Tuni dai shi ma sabon gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle, ya kuduri aniyar fito da hanyar sulhu, domin dakile kalubalen tsaro a jihar, inda ya gudanar da tarurruka da Fulani, da ‘yan sa kai, da sarakunan gargajiya, da kuma jami’an tsaro.
Domin karin bayani, saurar cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Murtala Faruk Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5